Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon babban sakataren hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf a gaban babbar kotu tarayya Abuja, kan tuhume-tuhume biyar.
Yusuf, wanda ya yi aiki a matsayin babban wakatare na NHIS tsakanin 2016 zuwa 2017, an zarge shi da yin amfani da ofishinsa wajen bai wa kansa wasu abubuwan da ba su dace baz da bayar da kwangiloli ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba.
Yayin zaman kotun, a yau Litinin Yusuf ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi lokacin da aka karanta masa, inda O.I. Habeeb, ya bukaci a ci gaba da tsare shi a hannun EFCC har sai an saurari bukatar belinsa.
Sabon labari: Mawallafin jaridar Nigerian Tracker ya zama ma’ajin kungiyar kafafen yada labaran Internet na Arewa
Sai dai alkalin kotun, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta ce “da zarar an gurfanar da wanda ake tuhuma, ya daina kasancewa a hannun EFCC.”
Daga nan ta ba da umarnin a tsare Yusuf a gidan yari na Kuje da ke Abuja har sai an saurari bukatar belinsa.
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairun 2025 domin ci gaba da shari’ar.













































