“Za’a cimma matsayar tattaunawar mafi karancin albashi” – Cewar Gwamnonin Najeriya

Gwamnonin, Najeriya, cimma, matsayar, tattaunawar, mafi, karancin, albashi
Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta tabbatarwa 'yan Najeriya da kungiyoyin kwadago cewa batun mafi karancin albashi zai samu sakamakon tattaunawar da ake yi...

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta tabbatarwa ‘yan Najeriya da kungiyoyin kwadago cewa batun mafi karancin albashi zai samu sakamakon tattaunawar da ake yi.

Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan wani taron gaggawa da aka yi tun da sanyin safiyar ranar Alhamis, wanda mukaddashin Daraktan yada labarai na kungiyar NGF, Ahmed Salihu ya sanyawa hannu.

Ya nuna cewa zaman ya tattauna kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa tare da amincewa da ci gaba da yin cudanya da masu ruwa da tsaki a harkar na cimma mafita mai yarda da juna.

Karin labari: VC: An zabi Farfesa Aisha Maikudi a matsayin mukaddashin shugaban jami’a

Gwamnonin sun amince da aiki da gudunmawar da ma’aikatar harkokin mata ke bayarwa wajen inganta daidaiton jinsi da karfafawa mata da kuma ci gaban zamantakewa a fadin Najeriya.

Majalisar ta tattauna kan sabon mafi karancin albashi na kasa. Gwamnonin sun amince da ci gaba da yin cudanya da manyan masu ruwa da tsaki domin cimma matsaya mai dacewa.

“Mun ci gaba da sadaukar da kai ga tsarin kuma muna ba da tabbacin cewa za a samu mafi kyawun albashi daga tattaunawar da ake yi.”

Karin labari: Kotu ta hana gwamnan Sakkwato korar Hakimai 10

Gwamnonin jihohi 36 sun bayyana muhimmancin da Bankin Duniya da Najeriya ke da shi na samar da ayyukan mata, tare da jaddada wajabcin aiwatar da shi a matakin jiha kamar yadda aka yi niyya tun da farko, ganin cewa jihohi ne ke da alhakin gudanar da aikin.

“Mu ‘yan kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) a taron da muka gudanar a yau, mun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasar nan.”

Mambobin sun bayyana aniyar ci gaba da bayar da tallafin da ake bukata don tabbatar da ingancin shirin a fadin kasar nan.

Karin labari: Shugaban kasar Kenya ya janye shirin haraji bayan gudanar da zanga-zanga

Haka zalika, mambobin sun samu bayani daga Mista Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin kasafin kudi na fadar shugaban kasa da sake fasalin haraji.

Ya bayyana ci gaban da aka samu dangane da manufofin kasafin kudi da garambawul na haraji. Ya nemi shawarwari da goyon bayan manyansu kan wasu shawarwari da za su yi tasiri kai tsaye ga matakin gwamnatin tarayya.

A karshe sun yi alkawarin bawa kwamitin goyon baya don tabbatar da nasarar aiwatar da wadannan sauye-sauye da kuma hada kai don magance duk wani kalubalen da ka iya tasowa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here