Wata ƙungiya a Kano ta ƙaddamar da gangamin dashen itatuwa don yaki da ɗumamar yanayi

WhatsApp Image 2025 10 16 at 16.00.39 750x430

Ƙungiyar ci gaban Bichi wato Fitilar Jama’ar Bichi ta bayyana aniyarta na ci gaba da yakar ɗumamar yanayi a yankin Bichi da ke jihar Kano ta hanyar gudanar da shirin dasa itatuwa a duk shekara domin kare muhalli da raya gandun daji.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Rilwanu Idris Malikawa Garu, ya bayyana haka yayin ƙaddamar da shirin a bana a kasuwar zamani ta Bichi, inda ya ce ƙungiyar ta samar da ɗaruruwan tsirrai da za a raba a sassa daban-daban na ƙaramar hukumar domin dasawa.

Alhaji Malikawa ya bayyana cewa wannan shiri ya fara ne a bara, kuma yana ɗaya daga cikin gudunmawar ƙungiyar wajen yakar ɗumamar yanayi, lalacewar ƙasa, gurbatar iska da kuma sauyin yanayi a yankin.

Ya yi kira ga shugabannin kasuwa da sauran wuraren da aka zaɓa da su kula da tsirran da aka dasa tare da tabbatar da sun tsira.

Shugaban ƙaramar hukumar Bichi, Alhaji Hamza Mai Fata, wanda jami’in kasuwar Bichi, Alhaji Garba Tukur, ya wakilta, ya yabawa ƙungiyar bisa namijin ƙoƙarinta wajen aiwatar da shirye-shiryen da ke amfani ga al’umma.

Hakazalika, Hakimin Bichi, Galadiman Kano, Alhaji Mannir Sunusi, ta bakin sakatarensa Malam Idi Shitu Malikawa, ya yi kira ga dagatai da masu unguwanni da su tallafa wa wannan shiri tare da aiwatar da irin sa a yankunansu.

A cikin jawabin da ya gabatar, malamin addini Ustaz Rabi’u Sadiq ya jaddada muhimmancin dasa itatuwa, yana mai cewa aikin yana da lada mai yawa a wurin Allah, domin yana ci gaba da amfanar da jama’a har bayan mutuwar mai dasa shi.

Shugaban kasuwar zamani ta Bichi, Alhaji Abubakar Bichi, ya gode wa ƙungiyar saboda zaɓar kasuwar a matsayin wurin ƙaddamar da shirin, tare da tabbatar da cewa za su kula da dukkan tsirran da aka dasa a kasuwar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here