Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana alhini bisa rasuwar Janar Abdullahi Mohammed Adangba (mai ritaya), wanda ya taɓa zama shugaban ma’aikata ga tsoffin shugabannin ƙasa Olusegun Obasanjo da Umaru Musa Yar’Adua.
Marigayi Janar Mohammed, wanda ya rasu yana da shekaru 86, ya taka rawar gani wajen gina tsarin tsaron ƙasa, musamman a lokacin da aka kafa tsohuwar Ƙungiyar tattabar da tsaron ƙasa, wadda daga bisani ta haifar da Hukumar Tsaron Cikin Gida (SSS), Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA), da Hukumar Leken Asiri ta Soja (DIA).
Haka kuma, ya taɓa rike mukamin gwamnan tsohuwar jihar Benue-Plateau tsakanin shekarar 1975 da 1976.
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayi Janar Mohammed a matsayin soja mai ladabi, ƙwararre kuma mai kishin ƙasa, wanda ayyukansa suka shafi tsawon shekaru na hidima ga ƙasar, tare da gudunmawar da ta taimaka wajen zaman lafiyar Najeriya da ci gaban gwamnati.
Ya bayyana cewa marigayin ya yi hidima ga ƙasa da mutunci, tsari, da tawali’u, wanda hakan ya bar gagarumin tasiri a hukumomin da ya yi aiki da su, musamman a fadar shugaban ƙasa, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara tsarin mulkin shugabanci.
Shugaban ƙasar ya taya iyalan marigayin, gwamnatin jihar Kwara, rundunar sojojin Najeriya, da duk iyalai kan wannan babban rashi mai girma.













































