Shugabancin ƙasa: Shekarar 2027 ba lokacin Kudu maso Gabas ba ne – Umahi

Dave Umahi old 750x430

Ministan ayyuka, Injiniya David Umahi, ya bayyana cewa yankin Kudu maso Gabas ya kamata ya nuna haƙuri dangane da burinsa na neman shugabancin ƙasar, yana mai cewa ba lokacin yankin ba ne a zaɓen 2027.

Umahi ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a ranar Lahadi a Abuja, inda ya jaddada muhimmancin adalci da ci gaba da tsarin mulki a shekara ta 2027, yana kuma yabawa ayyukan da Shugaba Bola Tinubu yake yi tun bayan hawansa mulki a 2023.

Ya ce tun kafin zaɓen 2023, gwamnoni 17 na Kudancin Najeriya sun haɗu a Asaba suka amince cewa dole ne shugabancin ƙasa ya koma yankin kudu, duk da bambancin jam’iyyunsu.

Sai dai daga ƙarshe wannan damar ta tabbata ga Shugaba Bola Tinubu, wanda shi ma ɗan kudu ne, don haka ba daidai ba ne a ce yanzu lokacin kudu maso gabas ya yi.

A cewarsa, Tinubu yana da wa’adin shekara takwas, wanda ke nufin cewa har zuwa shekara ta 2031 kafin a iya tunanin cewa yankin kudu maso gabas zai nemi shugabancin ƙasa.

Umahi ya ce hakan zai baiwa tsarin adalci da daidaito damar tabbata tsakanin sassan ƙasar.

Ya kara da cewa duk da cewa yankin kudu maso gabas ya sha fama da wariya a baya, yanzu shugaba Tinubu yana nuna adalci da kulawa ga kowa ba tare da la’akari da asalinsu ba.

Umahi ya ce duk da ƙarancin muƙamai da yankin ya samu, matsayin ministan ayyuka da yake rike da shi ya kai darajar manyan ministoci guda biyar saboda muhimmancin ayyukan da ake gudanarwa a yankin.

Ya bayyana wasu daga cikin manyan ayyukan da ake yi a yankin, ciki har da gyaran hanyoyin Enugu zuwa Onitsha da kudinsu ya kai Naira biliyan 350, aikin MTN na Naira biliyan 202, aikin CBC na Naira biliyan 150, da kuma hanyoyi da gadar da ake ginawa daga Ebonyi zuwa Benue, wanda darajarsu ta kai Naira biliyan 456.

Umahi ya ce duk waɗannan ayyuka suna nuna irin kulawar da gwamnatin Tinubu ke nunawa ga yankin, yana mai cewa mazauna kudu maso gabas ya kamata su nuna godiya ga shugaban ƙasa.

A ƙarshe, ya jaddada cewa duk da matsalolin da yankin ya fuskanta a baya, lokaci ya yi da za a mai da hankali wajen gane abubuwan da ke faruwa yanzu, domin a ci gaba da haɓaka yankin cikin haɗin kai da sauran sassan ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here