Sarkin Musulmi Ba Shi da Ikon Nada Kowa – Gwamnatin Sokoto

Gwamnan, Sokoto, Kotu, hana, korar, Hakimai
Wata babbar kotu a jihar Sakkwato karkashin mai shari’a Kabiru I. Ahmed ta bayar da takardar neman a ci gaba da shari’a mai lamba SS/M.290/2024 da SS/M.293...

Gwamnatin jihar Sokoto ta ce bisa tsarin mulki, Sarkin Musulmi ba shi da ikon nada kowa.

Da yake jawabi a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan dokar kananan hukumomi da masarautu ta Sokoto 2008, a ranar Talata, kwamishinan shari’a, Barista Nasiru Binji, ya ce dokar da ake da ita a jihar ta saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya ce sashe na 76(2) na dokar ya sabawa sashe na 5(2) na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima

“Sashi na 5 (2) na kundin tsarin mulkin kasa ya nuna cewa ikon zartarwa na nadawa a jihar yana hannun Gwamna ne kai tsaye ko ta hannun mataimakinsa ko kwamishinoni ko duk wani wakilin gwamnati da Gwamna ya ba shi.

 

“Don haka babu wani ikon da aka bai wa majalisar Sarkin Musulmi ta nada. Sashi na 76(2) na dokar kananan hukumomi da masarautu ta Sokoto ya baiwa majalisar sarkin musulmi ikon nada hakimai da gundumomi a jihar amma tare da amincewar gwamna mai ci.

“ sashin bai dace da kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima ba don haka ba zai iya tsayawa ba. Domin kuwa ikon nada shi ne na zartaswa kuma wa ke yin mulki, ba Gwamna ba? Wannan shi ne dalilin gyara. Domin gyara kuskuren da aka yi a baya,” inji shi.

A kan kudirin dokar tsawaita wa’adin shugabannin kananan hukumomi zuwa shekaru uku, shi ne a ba su damar yin aiki yadda ya kamata.

Daily Trust

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here