Kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta bayyana matukar damuwarta kan cece-kucen da ake tafkawa a majalisar dattawa ta 10 da ya shafi shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta tsakiya.
A cikin wata sanarwa da Farfesa Tukur A. Muhammad-Baba, sakataren yada Labarai na ACF ya fitar, ya ce, kungiyar ta damu da munanan zarge-zargen cin zarafi da Sanata Akpoti-Uduaghan ya yi, wanda ake ta tataunawa a kafafen yada labarai.
Bugu da kari, kungiyar ta nuna damuwarta kan yiwuwar nuna son kai ga Sanatocin Arewa, inda ta nuna cewa ‘yan majalisa daga Arewa ne kawai suke fuskantar takunkumi ciki har da dakatarwa a majalisar dattawan da ke yanzu.
Karin karatu: Na faɗawa Akpabio ya daina cin zarafin matata – mijin Natasha
ACF ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, a bayyane, da gaskiya kan zarge-zargen don tabbatar da adalci.
A cewar kungiyar dole ne majalisar Dattawa ta koma bakin aikinta na kafa doka, musamman a wannan lokaci da ‘yan Najeriya ke fama da tabarbarewar tattalin arziki.
Haka kuma ya kamata ‘yan majalisa daga Arewa a Majalisar Dattawa ta 10 su hada kai da Akpoti-Uduaghan don ganin an yi mata adalci da kuma girmama ta.
ACF ta ce, sunan majalisar dattijai ta 10 yana cikin hadari, kuma dole ne mambobinta su yi aiki ta hanyar da ta dace da nauyin da ke kansu.
A karshe kungiyar ta ACF ta bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su ba da fifiko ga kasa da kuma tabbatar da cewa majalisar dattawa ta ci gaba da tabbatar da amincin ta a gida da waje.