Rashin tsaro: Ƙungiyar gwamnoni ta kafa kwamiti ga hukumomin tsaro na tarayya

NGF Hope 750x430 (1)

Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta kafa wani karamin kwamiti da zai hada kai da shugabannin hukumomin tsaro domin magance matsalolin tsaro a kasar nan da nan.

Gwamna Hope Uzodinma ya bayyana hakan ne da sanyin safiyar ranar Alhamis yayin da yake karanta sanarwar bayan taro na biyu na kungiyar NGF da aka yi a daren Laraba a Abuja.

Sanarwar ta samu sa hannun shugaban kungiyar, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara.

Uzodinma ya ce, gwamnonin sun yanke shawarar ne sakamakon jin dadinsu na hanyoyin da ake amfani da su ta hanyar fasaha da Babban Hafsan Tsaro (CDS) ya gabatar a jawabin sa yayin taron.

“Gwamnoni sun nuna goyon bayansu ga manufofin shirin tare da jaddada muhimmancin amfani da hanyoyin fasahar wajen magance matsalolin tsaro a matakin jiha.

Labari mai alaƙa: Kungiyar Gwamnoni ta gana da babban Hafsan soji kan matsalolin tsaro

Gwamnonin sun kuma yaba wa CDS da sojojin Najeriya kan waɗannan kyawawan shawarwari da tsare-tsare,” inji shi.

Uzodinma ya kara da cewa, taron ya kuma samu jawabi daga ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa, kan yadda za a bullowa tattalin arzikin kasa ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihohi domin sake fasalin kasa.

Ya ce ministan ya zayyana ayyukan gina gidaje da ake ci gaba da yi a karkashin shirin sabunta muradu tare da ba da shawarar sake fasalin filaye don daidaita mallakar filaye da inganta tsaro da bunkasa kudaden shiga a cikin gida a fadin jihohi.

“Zauren ya kuma samu bayyani kan wani shiri na hadin gwiwa tare da Powercom Smart Grid Nigeria Limited (PSGN), da nufin farfado da bangaren rarraba wutar lantarki ta hanyar saka hannun jari masu zaman kansu.

“A karkashin yarjejeniyar da aka tsara, PSGN za ta dauki nauyin gudanar da ayyuka na zaɓaɓɓun kamfanonin rarraba wuta (Discos).

Dangiwa wanda ya yi magana tun farko a wata hira da manema labarai, ya ce an gabatar da shi ne domin sabunta wa gwamnonin shirin sabunta maradu na gwamnati mai ci.

Shima da yake nasa jawabin, Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce bai kamata a kalli kashe-kashe da hare-haren da ake kaiwa wasu jihohin a matsayin zargi ga gwamnonin ba, domin suna da takaitaccen rawar da za su taka wajen magance matsalolin tsaro.

Sani ya ce yayin da ya amince da maganar Majalisar Tsaro ta kasa ya kuma yi imanin cewa ya kamata hukumomin tsaro a Najeriya su kara kaimi da yin abin da ya dace.

Ya ce duk da cewa dole ne shugabanni su dauki nauyi, akwai bukatar masu ruwa da tsaki su hada kai tare da magance matsalar rashin tsaro (NAN).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here