Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ware guraben hajji 1,518 ga Jihar Jigawa don aikin hajjin 2025.
Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmad Labbo, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Dutse ranar Asabar.
Labbo ya ce an raba kashi 70 cikin 100 na guraben da aka ware ga kananan hukumomi 27 na jihar domin sayarwa ga masu sha’awar zuwa aikin hajji.
Ya ce kashi 30 cikin 100 na guraben an ajiye su har sai an kammala siyar da na farko da aka bai wa kowacce karamar hukuma.
Ya kara da cewa ana sa ran masu niyyar aikin hajji su biya Naira miliyan 8.4 a matsayin ajiyar kuɗi kafin sanarwar hukuma kan farashin aikin hajjin bana.
Labbo ya bukaci masu sha’awar aikin hajjin su gaggauta biyan kudin don ba wa hukumar damar kammala shirye-shiryen aikin hajjin da wuri.
Aikin Hajji, daya daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar, shine tafiya zuwa Makka da Musulmai daga sassa daban-daban na duniya ke yi duk shekara.