Alema na Masarautar Warri kuma mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Cif Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan, ya tabbatar da cewa ya fadawa Sanata Godswill Akpabio ya daina cin mutuncin matarsa.
Wannan dai na zuwa ne a kan takaddamar da ke tsakanin uwargidansa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio
Cif Uduaghan ya ce shiga tsakani da ya yi ya zama dole, sakamakon ya dade yana kawar da kai daga manyan zarge-zargen da ke tattare da su, wanda ya kamata ya shafi kowane mai hankali ga me da iyalinsa.
Karin karatu: Akpabio ya so ya kwanta da ni kafin ya bar ni in gabatar da ƙudiri – Natasha
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da dan kasuwar ya sanya wa hannu a daren ranar Asabar kuma ya rabawa wa manema labarai.
Ya ce ya gana da Akpabio ne bayan da matarsa wadda ita ce Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ta bayyana masa halin da take ciki a Majalisar Dattawa a karkashin Shugaban Majalisar.
“Da farko na yanke shawarar cewa zan daina yin tsokaci kan rikicin da ke faruwa tsakanin matata masoyiyata, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio. Duk da haka, abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun tilasta ni in fitar da wannan sanarwa.