Ministan da Tinubu ya tura wa majalisa ya faɗi a lokacin tantancewa

4adfbfa6 2dc0 4310 bdec 450efd60bea1
4adfbfa6 2dc0 4310 bdec 450efd60bea1

Ɗaya daga cikin ministocin da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tura wa Majalisar dokokin ƙasar domin tantancewa ya yanke jiki ya faɗi a zauren majalisar.

Ministan wanda ya fito daga jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal ya faɗi ne a daidai lokacin da ya kammala jawabi kan tarihin rayuwa da karatunsa.

Sai dai nan da nan aka ɗaga shi kuma aka zaunar da shi a kan kujera.

Majalisar dai ta shiga zaman sirri bayan faɗuwar sa.

Tun farko a lokacin da yake jawabi, Abbas ya shaida wa majalisar cewa ya yi matuƙar murnar damar da ya samu, kuma yanayi ne da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here