Mataimakin shugaban ƙasar Brazil ya sauka a Najeriya domin halartar tattaunawa

1750748954355 750x430

A yau Talata ne mataimakin shugaban kasar Brazil Geraldo Alckmin da mai dakinsa Maria Alckmin suka iso Najeriya domin halartar taro na kwanaki uku na tsarin tattaunawa tsakanin Najeriya da Brazil mai taken Strategic Dialogue Mechanism, SDM.

A yayin da tawagar ta sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Sanata Ibrahim Hadejia da ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dakta Jumoke Oduwole ne suka tarbe su.

Sauran jami’an gwamnati da suka tarbi tawagar sun hada da Ministan ma’aikatar bunkasa fannin Dabbobi Idi Maiha da Ministan Noma da samar da Abinci Sanata Abubakar Kyari, da dai sauransu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa, ziyarar tasu wani bangare na cikin harkokin diflomasiyya da kuma tabbatar da inganta fannin inganta harkokin ruwa a Kudu maso Kudancin Najeriya.

Ana sa ran zai samar da gagarumin ci gaban manufofi a bangarori da dama.
Da ya ke jawabi a wata takaitacciyar liyafar da aka yi a filin jirgin, Sanata Ibrahim Hadejia ya bayyana ziyarar a matsayin “lokaci mai matukar muhimmanci a cikin ajandar sabunta manufa ta Najeriya.”

Ya kuma jaddada muhimmancin dabarun zurfafa dangantaka da Brazil.

Taron na kwanaki uku zai karkare ne wajen rattaba hannu kan yarjeniyoyi sama da 30 na fahimtar juna a sassa masu muhimmanci.

Bangarorin sun hada da; hadin gwiwar tsaro, musayar fasahar noma, hadin gwiwar makamashi, da shirye-shiryen musayar al’adu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here