Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa ƙasar Brazil domin wakiltar shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu a taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 30, wanda ake kira “COP 30,” da za a gudanar a ƙasashen Kudancin Amurka.
An shirya taron ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, tare da haɗin gwiwar wasu ƙasashe, daga ranar 6 zuwa 7 ga watan Nuwamba, a birnin Belém, babban birnin jihar Pará da ke cikin dajin Amazon.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Shettima, Stanley Nkwocha, mataimakin shugaban ƙasa zai haɗu da shugabannin ƙasashe, abokan ci gaba, da manyan ’yan kasuwa a taron mai taken “Ayyukan sauyin yanayi da aiwatarwa,” inda za a mayar da hankali kan kariya ga dazuzzuka, bambancin halittu da adalcin yanayi.
A rana ta farko, Shettima zai halarci zaman shugabanni na babban taro inda zai gabatar da jawabin Najeriya kan matakan da ƙasar ke ɗauka wajen sauyin yanayi.
Haka kuma zai halarci ƙaddamar da asusun “Tropical Forest Forever Fund,” da kuma taron tattaunawa ta musamman ƙarƙashin shugabancin shugaba Lula kafin ya shiga taron girmamawa na shugabanni da shugaban ƙasar Brazil zai dauki nauyi.
A rana ta biyu, Shettima zai shiga wasu taruka biyu da shugaban ƙasar Brazil zai jagoranta kan batun canjin makamashi da kuma nazarin yarjejeniyar Paris, inda za a tattauna kan gudunmawar ƙasashe da hanyoyin samar da kuɗaɗen tallafi.
A gefen taron, Shettima zai gudanar da wasu tattaunawa ta musamman don inganta shiga Najeriya cikin kasuwancin carbon, wanda ake sa ran zai iya samar wa ƙasar kuɗaɗe tsakanin dala biliyan 2.5 zuwa 3 a shekara a cikin shekaru goma masu zuwa.
Bayan kammala taron COP 30, Shettima zai wuce birnin Brasilia domin ziyarar hadin gwiwa ga mataimakin shugaban ƙasar Brazil, Geraldo Alckmin, wanda ya ziyarci Najeriya a watan Yuni da ya gabata, inda aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi a fannoni da dama ciki har da tsaro, noma, makamashi da musayar al’adu.
An tsara cewa mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima zai dawo Najeriya bayan kammala ayyukansa a Brazil.













































