Majalisar wakilai za ta koma bakin aiki aranar 20 ga satumba

Gbajabiamila
Gbajabiamila

Majalisar wakilai za ta koma zamanta a ranar 20 ga Satumba awani zauren wucin gadi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da magatakardar majalisar Yahaya Danzaria ya fitar akarshen mako a Abuja.

Danzaria ya ce la’akari da gyare gyaren da ake gudanarwar a tsohon zauren majalisar, ana sa ran mambobin za su koma zama a sabon dakin da aka gyara a sabon ginin mai dauke da kujeru 118 kacal.

Ya ce an fadada sabon zauren Majalisar ta hanyar samar da bene mai karfin kujeru 236, inda ya kara da cewa an hada dakunan da sautukan na’urar lantarki da manyan alluna domin samar da tsare tsare.

Sai dai ya ce babu wasu kujeru da aka kebe baya ga kason shugabanni da manyan hafsoshi.

“Hakazalika yana da muhimmanci a lura cewa saboda wannan tsari ne na wucin gadi da aka tsara ba wani tanadi da aka yi wa shugabanni da mataimakan ahugabannin majalisa saboda rashin sarari.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa majalisar a ranar 20 ga watan Yuli ta tafi hutun watanni biyu gabanin zagayen karshe na Majalisa ta 9.

Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila a ranar 14 ga watan Satumba ya yi kira da a gaggauta kammala aikin gyaran majalisar dokokin da ake yi a yanzu gabanin wa’adin mika mulki ga watan Agustan 2023.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here