Majalisar wakilai ta janye amincewa da ƙudurin cire rigar kariya ga mataimakin shugaban kasa da gwamnoni bayan karatu na biyu

Reps Reps 750x430 (1)

Majalisar wakilan Najeriya ta janye matakin da ta ɗauka na amincewa da karatu na biyu na ƙudurin dokar da ke neman cire rigar kariya ga mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakansu.

Hakazalika majalisar ta janye amincewa da ƙudurin da ke neman a soke hukuncin kisa ga masu aikata laifi a ƙasar.

Ƙudurorin biyu na cikin ƙudurori 42 da suka tsallake karatu na biyu a jiya Laraba.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudurin janyewar.

Labari mai alaƙa: Ƙudirin dokar cirewa mataimakin shugaban kasa da gwamnoni rigar kariya ya tsallake karatu na biyu

Mataimakin kakakin majalisar Benjamin Kalu ya ce an ɗauki matakin janyewar ne domin bayar da damar yin muhawara kan ƙudurorin.

Ƙudurorin na daga cikin gwamman ƙudurorin da majalisar ke nazari a kansu, a wani ɓangare na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin ƙasar na shekarar 1999.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here