A wani gagarumin yunkuri na inganta hadin gwiwar ilimi da kuma cudanya a duniya, Jami’ar tarayya, Kashere (FUK) a Jihar Gombe, ta kulla yarjejeniyar fahimtar juna da Jami’ar Beaconhouse, Lahore, Pakistan.
SolaceBase ta ruwaito cewa an tsara yarjejeniyar ne a ranar Talata a Lahore, tare da shugaban jami’ar FUK Farfesa Umaru Pate, da takwaransa na jami’ar Beaconhouse, Farfesa Mojeed Hossin, sun kuma sanya hannu kan yarjejeniyar.
Da yake jawabi a wurin rattaba hannu kan yarjejeniyar, Farfesa Pate ya bayyana hadin gwiwar a matsayin wani muhimmin mataki na bunkasa ilimi a duniya. “Wannan yarjejeniya za ta bude kofofi don musayar malamai da dalibai, ayyukan bincike na hadin gwiwa, da kuma raba albarkatun ilimi tsakanin cibiyoyinmu,” in ji shi.
A nasa bangaren, Farfesa Hossin ya jaddada tasirin hadin gwiwar da ke tattare da musanyar ilimi da inganta bincike. “Jami’ar Beaconhouse ta himmatu wajen samar da hanyar sadarwa ta ilimi a duniya, kuma wannan hadin gwiwa da Jami’ar tarayya, Kashere, ta yi daidai da manufarmu ta kirkire-kirkire da dunkulewar kasa da kasa,” in ji shi.
Yarjejeniyar ta ƙunshi nau’ikan shirye-shiryen ilimi, gami da shirye-shiryen musayar ɗalibai da malamai, bincike na haɗin gwiwa a fannoni daban-daban, yunƙurin gina ƙarfin haɓaka ma’aikata da tarukan haɗin gwiwa, tarurrukan karawa juna sani, da wallafe-wallafe.
Dukan cibiyoyin sun bayyana fatansu cewa haɗin gwiwar zai ƙarfafa amonsu a duniya tare da haɓaka ƙwarewar ilimi.
Yarjejeniyar ta fara aiki nan take, tare da tattaunawa kan aiwatar da tsarin farko na shirye-shiryen hadin gwiwa.