Hukumomi a yankin Tigray na arewacin ƙasar Habasha sun sanar da korar tsofaffin mayaƙan sa kai 100,000 bisa yarjejeniyar zaman lafiyar Pretoria ta shekarar 2022 a cewar wani rahoto da jaridar Addis Standard mai zaman kanta ta fitar.
Shugaban rikon kwarya na yankin na Tigray, Getachew Reda, ya jaddada kudirin gwamnatin ta Tigray na aiwatar da yarjejeniyar Pretoria, duk kuwa da kalubalen da ake fuskanta kamar rashin isassun kayan aiki na gyarawa da kuma mayar da mutanen da aka kora.
Karin labari: Dakarun Djibouti sun fice daga tsakiyar Somaliya saboda rikicin cikin gida
A baya dai Getachew Reda ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta kori tsofaffin mayakan sa kai sama da 270,000 ba har sai an kammala aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a watan Nuwamban 2022 tsakanin gwamnatin tarayya da tsohuwar ‘yan tawayen Tigray People’s Liberation Front (TPLF).