Hukumar karbar korafi da yaƙi da rashawa ta Kano za ta binciki masu ɓoye kayan abinci

Hukuma, rashawa, cin hanci, bincike, boye, abinci
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta gargadi ‘yan kasuwar da ake zargi da boye kayan abinci da su daina. Hukumar ta ce bayan...

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta gargadi ‘yan kasuwar da ake zargi da boye kayan abinci da su daina.

Hukumar ta ce bayan korafe-korafen da ta karba daga mutane daban-daban ta umarci jami’anta su fara bincike wuraren da ake zargin an makare manyan sito-sito da kayan abinci.

Karanta wannan: “Sauye-sauye 3 da zan samar a hukumar fina-finan Najeriya” – Ali Nuhu

Shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce sun gano cewar boye kayan na daga cikin abubuwan da suke kara tsadar kayan masarufi a Kano, inda ya ce duk mutumin da suka kama to zai dandana kudarsa.

Ana dai ta zarge-zargen cewa manyan ‘yan kasuwa na boye kayan masarufi har sai ya yi tsada su fito da shi su sayar, wani abu da ake ganin yana taimakawa wajen kara dagula lamarin tsadar kayan na masarufi a Najeriya.

Da yake jawabi ga manema labarai a ofishinsa a ranar Alhamis, Shugaban Hukumar, Barr. Muhuyi Magaji Rimin-Gado, ya ce ya dace a yi hakan a ci gaba da kokarin rage radadin tattalin arzikin da ‘yan kasar ke fama da shi inda ya sha alwashin gurfanar da su tare da kwace kayayyakin da aka boye.

Karanta wannan: Tsoho dan shekara 84 ya kashe matar sa bisa kin yin kwanciyar aure dashi – Yan sanda

SOLACEBASE ta rawaito cewa shugaban ya yi gargadin cewa, “Ina so in bayyana a sarari cewa mun kuma sa ido da kuma bayanan sirri kan wanda ake zargi, kuma idan aka gano irin wadannan munanan ayyuka, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kulle rumbun ajiyar da abin ya shafa, mu kwace kadarorin kuma a kai su kotu.”

Ya ba da tabbacin cewa “Bari in bayyana karara cewa duk wanda ya ba mu damar kwace kadarorinsa ba zai dawo da shi ba, kuma a shirye muke mu kai ga kotun koli.”

Ya bayyana cewa “Bincike ya gano tasirin da wasu abubuwa ke yi a cikin tsarin, kuma kuna iya tambayar kanku menene alakar Forex da kayan amfanin gona kamar wake da gari da kuma masara tare da hatsi da sauransu”.

Karanta wannan: Naira ta ragu zuwa 1,500 a kasuwar canjin kudade

‘Yan kasuwa dai a Kano da ma Najeriya na musanta zarge-zargen da ake yi musu, inda ko a makon da ya gabata sai da gamayyar kungiyar ‘yan kasuwa a birnin Kano ta yi barazanar rufe kasuwanci saboda tsadar abubuwa.

Ko a makon da ya gabata sai da daruruwan al’ummar birnin Minna na jihar Neja suka yi zanga-zangar nuna damuwa kan yanayin tsananin rayuwa da ake ciki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here