*Hukumar NYSC ta nada sabon jami’in yada Labaranta*

Majalisa, NYSC, tallafawa, kudurin, asusun, hukumar, kafa
Majalisar dattijai ta amince da wani kudirin doka da ke neman a kafa asusun tallafawa masu yi wa kasa hidima NYSC. Ƙudurin dokar wanda Sanata Yemi Adaramodu...

Hukumar kula da Masu yiwa kasa hidima ta NYSC, ta nada Mista Eddy Megwa a matsayin sabon babban Daraktan Yada Labaranta.

Eddy Megwa ya maye gurbin Mrs Adenike Adeyemi, wacce ta kammala aiki a watan Nuwambar da ya gabata.

Megwa, wanda ya taba zama mataimakin daraktan sashen yada labarai tsawon lokaci, har zuwa lokacin da aka nada shi a matsayin babban jami’in gudanarwa na sakatariyar hukumar ta jihar Legas.

A cikin sanarwar da Hedikwatar hukumar ta NYSC ta fitar, Megwa ya kammala karatun digiri ne a Jami’ar Ilorin a shekarar 1989.

Ya kuma fara aiki a hukumar cikin shekarar 1990 a matsayin Jami’in Watsa Labarai, bayan shafe shekara guda yana hidima ga kasa.

Sanarwar ta kuma bayyana sabon Kakakin hukumar ta NYSC a matsayin gogaggen dan kishin kasa kuma mai mutunta al’adu da kabilu wanda kuma ya halarci kwasa-kwasai da dama a ciki da wajen Najeriya.

Kafin yanzu, Megwa ya yi aiki a Sakatariyar hukumar ta NYSC a jihohin Ribas da Anambra da Yobe sai Borno da kuma Benue a matsayin yada labarai.

A shekarar 2004, an nada shi a matsayin mai taimakawa jami’in kula da masu yi wa kasa hidima na kasa, mukamin da ya rike har zuwa shekarar 2010 inda aka mayar da shi sashin hulda da jama’a na Hedikwatar hukumar dake Abuja.

A shekarar 2019, an nada shi babban jami’in hukumar na Jihar Cross River sannan a shekarar 2020 aka mayar da shi Sakatariyar hukumar dake Jihar Legas a matsayin Shugaban Hukumar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here