Hukumar kula da harkokin ‘yan sanda ta kasa a ranar Juma’a ta kara wa mataimakan sufeto janar na ‘yan sanda Bakwai (AIGs) matsayi zuwa mataimakan sufeto janar na ‘yan sanda (DIG).
Hukumar ta bayyana cewa karin mukaman ya biyo bayan cancanta, matsayi na aiki, tarihin hidima da kuma sakamakon jarabawar rubutu da hirar baki da aka gudanar a hedikwatar PSC da ke Abuja, a wani mataki na ƙarfafa tsarin jagoranci na rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Sabbin DIG din sun hada da Zachariah Fera Achinyan wanda a baya yake AIG na Zone 4 a Makurdi, Zango Ibrahim Baba wanda a baya yake AIG na sashen kayan aiki da samarwa, da Isyaku Mohammed wanda a baya yake AIG mai kula da makamai a hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke Abuja.
Sauran sun hada da Margaret Agebe Ochalla wadda a baya take AIG a FCID Annex Lagos, Mohammed Abdul Sulaiman wanda a baya yake AIG mai kula da asusun kudi da kasafin kudin rundunar ‘yan sanda a hedikwata, Kenechukwu Onwuemelie wanda a baya yake AIG na Zone 15 a Maiduguri, da kuma Umar Shehu Nadada wanda a baya yake AIG na Zone 14 a Katsina.
Hukumar ta bayyana cewa karin mukaman ya biyo bayan karin mukamin DIG Fayoade Adegoke zuwa cikakken matsayi na DIG, wanda yanzu zai shiga cikin tawagar gudanarwar rundunar ‘yan sanda.
A cewar hukumar, karin mukaman ya zama dole domin cike guraben da suka biyo bayan ritayar DIG guda Takwas da a baya suke rike da wadannan muhimman mukamai.
Shugaban PSC, DIG Hashimu Salihu Argungu mai ritaya, ya taya sabbin DIG din murna tare da kira gare su da su yi aiki daidai da bukatun sabbin mukamansu tare da ba fifiko ga tsaron kasa da kuma kyakkyawar hulda da hukumar domin ci gaban rundunar ‘yan sandan Najeriya.













































