Hukumar EFCC Ta Kaddamar Da Bincike Bayan Da Wani Jami’in ta ya kashe kansa

EFCC Operatives

Wani jami’in hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ya kashe kansa a gidansa da ke Abuja.

Ba a bayyana sunan ma’aikacin wanda ya rasu a ranar Litinin ba, sai dai cewa marigayin mamba ne na Course 5 na kwalejin hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, a ranar Talata ya shaidawa manema labarai cewa ana gudanar da bincike don gano yadda abun ya faru.

Mista Oyewale ya kara da cewa hukumar zata bincike wasu abubuwan da suka hada da matsalar tabin hankali da kalubalen iyali da ka iya sanya ma’aikacin ya kashe kansa.

Ya kara da cewa Hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ba ko kuma ta bayyana sunan jami’in har sai an kammala bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here