Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya amince da dawo da ayyukan sadarwa a Gusau babban birnin jihar daga yau Juma’a 1 ga watan Oktoba.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a yau Juma’a mai dauke da sa hannun mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan wayar da kan jama’a da harkokin kafafen yada labarai da harkokin kafafen sadarwa, Malam Zailani Bappa.
Ta cikin sanarwar Zailani Bappa ya ce, dawo da ayyukan sadarwa a babban birnin jihar ya biyo bayan manyan nasarorin da aka samu a yaƙi da ƴan bindiga a jihar.
Ya kara da cewa dawo da hanyoyin sadarwar a Gusau zai sauƙaƙa wahalhalun da kamfanoni masu zaman kansu da na gwamnati ke fuskanta a harkokin kasuwancin su na yau da kullun.
Haka kuma ya ce, “Gwamnatin jihar ta ga dacewar sassauta matakin ne bayan da jami’an tsaro suka samu nasarar fatattakar ɓata garin da suka addabi jihar da ayyukan ta’addanci”.
A cewarsa, gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa kuma za ta sanar da ƙarin yanke shawara bisa matakan da ta ke ɗauka.
Haka kuma ya ƙara da cewa, zuwa yanzu an samu nasarar magance kimanun kaso 80 na ayyukan ta’addanci da jihar ke fama da shi.











































