Gwamnatin tarayya ta sake jaddada ƙudirinta na inganta walwalar malamai

A teacher doing his work

Gwamnatin tarayya ta sake tabbatar da aniyar ta na ci gaba da inganta walwalar malamai da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakanin su domin inganta koyarwa a faɗin ƙasar.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana haka a Abuja yayin bikin kammala ranar Malamai ta Duniya ta shekarar 2025 da kuma bayar da kyaututtukan Shugaban Ƙasa ga malamai da makarantu masu hazaka.

Ya ce taken bikin na bana “Sake fasalin koyarwa a matsayin tabbatar da haɗin gwiwa,” wanda hakan ya yi daidai da shirin gyaran tsarin ilimi na ƙasa da kuma ƙoƙarin duniya da hukumomin UNESCO, ILO, UNICEF da ke jagoranta.

Karanta: Sojojin sun musanta rahoton cewa ƴan bindiga sun mamaye su a Kwara

Alausa ya jaddada cewa malamai ginshiƙin ci gaban ɗan Adam ne da gina ƙasa, don haka sakawa da ƙarfafa su wata hanya ce ta saka jari a inganta ilimi, hazakar ɗalibai, da ci gaban ƙasa baki ɗaya.

Ya bayyana cewa ma’aikatarsa ta aiwatar da manufofi da dama don farfaɗo da harkar koyarwa, ciki har da manufofin Malamai na Ƙasa, da nufin ƙarfafa gwiwa da tallafawa malamai ta hanyar amfani da fasahar sadarwa wajen haɗa su da abokan aikinsu a faɗin ƙasar.

Ministan ya ce hukumomi kamar Hukumar yiwa Malamai rijista ta Najeriya (TRCN), Cibiyar Malamai ta Ƙasa (NTI), da Hukumar Ilimin Firamare ta Ƙasa (UBEC) na ci gaba da aiki tare domin tabbatar da ci gaban ƙwarewa da bin ƙa’idojin aikin koyarwa.

Ya ƙara da cewa koyarwa ba ta kamata ta kasance aikin mutum ɗaya ba, domin cigaban ilimi a yau na buƙatar haɗin kai, amana da raba alhakin aiki a tsakanin malamai.

Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta bayyana cewa ma’aikatar tana aiwatar da shirye-shirye da dama don ƙarfafa haɗin kai da haɓaka ingancin malamai, ciki har da kafa ƙungiyoyin koyo na malamai (PLCs) a makarantu daban-daban.

Ita ma ta ce waɗannan shirye-shiryen na nufin tabbatar da ƙwarewar malamai, da ƙarfafa ƙima da darajar koyarwa, tare da tabbatar da ingantaccen sakamako ga ɗalibai.

Karin labari: Hukumar NERDC ta ziyarci Jami’ar KHAIRUN domin inganta haɗin gwiwa

Shugaban ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT), Kwamared Audu Amba, ya jaddada cewa haɗin kai a tsakanin malamai zai taimaka wajen inganta tsarin koyarwa, ƙarfafa dangantaka, da gina tsarin ilimi mai ɗorewa da adalci.

Sai dai ya nuna damuwa kan yadda gwamnati ba ta aiwatar da dukkan fa’idodin da tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari ya amince da su don tallafa wa malamai ba, inda ya roƙi gwamnatin tarayya da jihohi su tabbatar da cikakken aiwatar da su domin ƙarfafa aikin koyarwa.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here