Gwamnatin Tarayya ta bayyana masu ɗaukar nauyin Sunday Igboho

Sunday Igboho
Sunday Igboho

Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya ce Gwamnatin Tarayya ta gano cewa babban mai daukar nauyin dan taratsin kafa yankin yarbawa, Sunday Igboho dan Majalisar Tarayya ne.

Malami ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai ranar Juma’a a Abuja

A cewar Malami, kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa ya bankado yadda Igboho ya samu kudade daga asusun banki 43, daga bankunan tara.

“Gwamnatin Tarayya ta karbi rahoton masu daukar nauyin Adeniyi Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho. Rahoton ya bayyana cewa Sunday Igboho Darakta ne a kamfanin Adesun International Concept Limited wanda aka yiwa rajista ranar 23 ga Afrilu, 2010.

“Adesun International Concept Limited kuma yana da Oladele Oyetunji da Aderopo Adeyemo a matsayin Daraktoci. Sunday Igboho yana da alaƙa da asusun banki 43 a bankuna 9 a cewarsa

Malami yace “An gano babban mai dauka nauyin ‘yan awaren dan Majalisar Tarayya a Majalisar Dokoki ta kasa ne. Jimlar Naira Miliyan Dubu Ashirin da Bakwai, Miliyan Dubu Arba’in da biyar Kawai (N127, 145,000.00) Igboho ya karba daga masu daukar nauyinsa a tsakanin 22 ga Oktoba 2013 zuwa 28 ga Satumba 2020 ta asusun Adesun International Concept Ltd.

“an kuma sanya Adadin jimlar miliyan dari biyu da saba’in da uku, da dubu dari da casa’in da takwas, da dari biyu kacal (N273,198,200.00) a asusun Sunday Igboho tsakanin 15 ga Maris, 2013 zuwa 11 ga Maris, 2021.

“Bincike ya nuna cewa Adesun International Concept Ltd (mallakar Igboho) ya tura naira miliyan goma sha biyu da dubu dari bakwai da hamsin (N12, 750,000) ga kamfanin Abbal Bako & Sons.

“idan za a iya tunawa Abbal Bako & Sons da mai tallata shi Abdullahi Umar Usman ana zargin su da tallafawa ‘yan ta’adda.

Ana kuma zargin Abdullahi Umar Usman da alaƙa da SURAJO ABUBAKAR MUHAMMAD (wanda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a Hadaddiyar Daular Larabawa bisa zargin ba da tallafin ta’addanci ga Boko Haram.

Malami yace “Rahoton ya gano alaƙar kasuwanci tsakanin Adesun International Concept Ltd (mallakar Igboho) da wasu kamfanonin gine -gine da kasuwanci da sauransu.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here