Gwamnatin Kano ta dauki sabbin jami’an Hukumar Hisbah sama da dubu uku

Hisbah Kano Kiyawa
Hisbah Kano Kiyawa

Gwamnatin jihar Kano ta dauki sabbin jami’an Hisbah guda 3,100 aiki a fadin kananan hukumomin jihar 44 da nufin kara karfin ma’aikatan hukumar.

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana hakan neranar Asabar yayin bikin rufe taron horar da jami’an Hisbah 270 da aka gudanar a sansanin masu kidimar kasa dake Kusalla a karamar hukumar Karaye.

A wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan Hassan Musa Fagge ya fitar, ya ce makasudin bayar da horon shi ne karfafa kwazon jami’an hukumar domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Sanarwar ta ce, horon ya gano kwararrun da suka dace wadanda za su iya taimakawa wajen magance matsalolin zamantakewar da ake fama da su a halin yanzu ta hanyar dabarun zamani da ka’idojin gudanar da aiki da hukumar Hisbah ke da su.

Gwamnan ya kuma yabawa hukumar ta Hisbah bisa gudunmawar da take bayarwa wajen inganta harkar tsaro a jihar, amma duk da haka ya bukaci jami’an su yi amfani da abin da aka koya musu a lokacin horon domin gudanar da aiki mai inganci.

Tun da farko, babban kwamandan hukumar, Ustaz Haruna Ibn Sinah ya bayyana cewa jami’an 270 sun baje kolin kyawawan halaye da kwazo tare da jajircewa a lokacin horon.

Ya kara da cewa nan da makwanni 2 masu zuwa hukumar zata sake haras da wasu rukunin jami’an 900 a karo na biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here