Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Dakta Suraj Sulaiman a matsayin sabon shugaban hukumar Ƙididdiga ta Jiha.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa an naɗa Dakta Sulaiman ne bayan karewar wa’adin tsohon shugaban Farfesa Aliyu Isa Aliyu, wanda aka naɗa a matsayin Kwamishinan harkokin Kiwo.
Gwamna Yusuf ya umarci a gudanar da bikin mikawa da karɓar aiki tsakanin tsohon da sabon shugaban hukumar a tsakanin Litinin da Juma’a na wannan mako.
Karanta: Shugaba Tinubu ya koma Abuja bayan ziyarar aiki a Legas
Sanarwar ta bayyana Dakta Sulaiman a matsayin masani mai ƙwarewa a fannin lissafi da bincike, wanda ke da gogewa mai zurfi a fannin koyarwa da nazarin bayanai.
Sanarwar ta kara da cewa Sulaiman ya yi digirin digirgir ne a fannin lissafi daga Jami’ar Teknologi Malaysia, digiri na biyu a Jami’ar Yasar da ke Turkiyya, sannan ya yi digirin farko a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano da ke Wudil.
Gwamna Yusuf ya taya sabon shugaban murna, yana mai bayyana amincewarsa da cewa zai taimaka wajen ƙarfafa tsarin sarrafa bayanai a jihar, tare da jaddada cewa sahihan bayanai suna da muhimmanci wajen tsara manufofi, tabbatar da gaskiya da kuma samun ci gaba mai ɗorewa a Kano.













































