Ganduje ya kafa kwamatin da zai yi binkice kan dalilin da haifar da rushewar ginin bene a kasuwar sayar da wayoyi ta Beruit

IMG 20220830 WA0189
IMG 20220830 WA0189

Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamatin da zai yi binkice kan dalilin da haifar da rushewar ginin bene a kasuwar sayar da wayoyi ta Beruit.

Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan ga manema labarai, bayan kammala taron majalisar zartarwa da ya gudana a gidan gwamnatin jihar Kano.

Jaridar Solacebase a ranar Talata ta rawaitu cewa ginin benen da ya rushe a kasuwar sayar da wayoyi ta Beirut, ya kashe mutane biyu da kuma jami’in hukumar KEDCO.

Garba ya ce Kwamatin zai aiki ne a tsawun sati daya ya kuma bada rahotan sa, domin daukar matakin da ya dace da gaggawa.

Membobin kwamatin su ne Engr. Rabiu Sulaiman Bichi wanda shine shugaban kwamatin, Engr. Idris Wada, M.A . Lawan, Engr. Mansur Ahmed, da kuma Dakta Kabir Ibrahim Getso.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here