Cikin Hotuna: Gwamnatin Kano ta rufe otal guda 10 saboda karya ƙa’idoji

WhatsApp Image 2025 10 10 at 17.24.24 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta rufe otal guda goma a faɗin jihar bisa zargin karya ƙa’idojin aiki da kuma rashin bin ɗa’a kamar yadda dokokin gwamnati suka tanada.

Mai taimaka wa gwamna na musamman kan harkokin labarai a hukumar yawon buɗe ido ta jihar, Ibrahim Adam Bagwai, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

Bagwai ya ce cikin otalan da abin ya shafa akwai Sarina Suites, Horizon Hotel, Blue Spot Hotel, da wasu otal guda bakwai.

WhatsApp Image 2025 10 10 at 17.24.25 1 WhatsApp Image 2025 10 10 at 17.24.23 1 WhatsApp Image 2025 10 10 at 17.24.25 2 WhatsApp Image 2025 10 10 at 17.24.25

Ya bayyana cewa matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa duk cibiyoyin yawon buɗe ido da otal-otal suna aiki daidai da dokokin da aka kafa tare da kiyaye ɗabi’a da tsaftar jama’a.

Ya ƙara da cewa hukumar yawon buɗe ido ta jihar za ta ci gaba da sa ido kan otal da wuraren hutu domin tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro, tsafta da daidaiton aiki, tare da kare mutuncin jihar a idon jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here