Ci gaban da aka samu a harkar ilimi zai iya lalacewa matukar ƙungiyar ASUU ta ci gaba da yajin aiki – NANS

National Association of Nigerian Students NANS 640x430

Ƙungiyar ɗaliban Najeriya ta kasa (NANS) ta bayyana damuwarta da cewa, ci gaban da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta samu a bangaren ilimi na iya lalacewa idan ba a dakatar da yajin aikin ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ba.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da shugaban ta na kasa, Kwamared Olushola Oladoja, ya fitar, inda ta ce ta gudanar da bincike kan dalilan rikicin da ya barke, tare da kira ga ɓangarorin biyu da su zauna su sasanta matsalar cikin gaggawa.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta samar da ci gaban da bai taɓa faruwa ba tun bayan dawo da mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, inda aka samu tsawon shekaru biyu na karatu ba tare da katsewa ba.

Hakan, a cewar ƙungiyar, ya faru ne sakamakon manufofi da dama da gwamnati ta ɗauka don inganta ilimi da walwalar ɗalibai da malamai.

Karanta: Darasin Lissafi ba zai zama dole ba ga ɗaliban ilimin fasaha masu neman shiga jami’a – gwamnatin tarayya

Daga cikin wadannan manufofi akwai kafa Asusun Lamunin Ilimin Najeriya (NELFUND) domin ba ɗalibai damar karatu ba tare da cikas na kuɗi ba, cire ma’aikatan jami’o’i daga tsarin IPPIS, janye manufar maida kaso 40% na kuɗaɗen da jami’o’i ke tara zuwa baitul-mali, da kuma bada tallafin musamman ta hukumar TETFund don gina sabbin gine-gine da tsaro a jami’o’i.

Haka kuma, gwamnati ta kaddamar da tsarin ilimin sana’o’i da fasaha kyauta tare da biyan ɗalibai ƙananan kuɗaɗe kowane wata, domin rage rashin aikin yi da ƙara wa matasa ƙwarewar da za su dogara da ita.

Sai dai, NANS ta nuna damuwa cewa rikicin da ke tsakanin gwamnati da ASUU na iya rushe wannan cigaba, inda ta ce matsalar ta samo asali ne daga rashin fahimta da kuma gazawar bin yarjejeniyar da aka cimma tun farko.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa bincikenta ya nuna cewa ASUU ta nuna haƙuri, yayin da ma’aikatar ilimi da ta kwadago ke ƙoƙarin aiwatar da yarjejeniyar, amma har yanzu ba a ga cikakken sakamako ba.

NANS ta bukaci gwamnati da ta kira taron sulhu cikin gaggawa, domin duka ɓangarorin sun bayyana shirinsu na halarta idan aka sake tsara shi yadda ya dace.

NANS ta kuma bai wa gwamnati da ASUU wa’adin kwanaki bakwai su warware rikicin, domin gujewa katse karatu da tsawaita lokacin ɗalibai a jami’o’i.

Ta kuma bukaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani kai tsaye, don kaucewa lalacewar cigaban da aka samu a karkashin gwamnatin Sabuwar Fata.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here