Bilbis Na PDP Ya Ragargaje Marafa A Kujerar Sanatan Zamfara ta Tsakiya.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana ‘yan takarar kujerar Sanatan Zamfara ta tsakiya na jam’iyyar PDP, Aliyu Ikira Bilbis, a matsayin wanda ya lashe zaben.

Aliyu Ikira Bilbis ya doke abokin hamayyarsa Kabiru Marafa na jam’iyyar APC.

Da yake sanar da sakamakon zaben, jami’in zabe na mazabar Zamfara ta tsakiya Farfesa Kabiru Abdullahi na Jami’ar Tarayya Gusau, ya ce Alhaji Ikira Aliyu Bilbis na PDP ya samu kuri’u 102,866 a kan abokin takararsa Sanata Kabiru Garba Marafa wanda ya samu kuri’u 91,216.

Farfesa Abdullahi ya ce Ikira Bilbis na PDP bayan ya cika sharuddan doka kuma ya samu kuri’u mafi rinjaye an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Idan za a iya tunawa, a ranar 28 ga Fabrairu, 2023 jami’in zabe na wannan zaben Sanata, Farfesa Ahmad Galadima ya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba sakamakon soke sakamakon zaben da aka yi.

Hakazalika, an bayyana ‘yan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wadanda suka lashe zaben majalisar wakilai da aka gudanar a mazabar Gusau/Tsafe da Gummi/Bukkuyum na tarayya.

A Gusau/Tsafe Kabiru Amadu Maipalace na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 63,589 inda ya doke tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Sanusi Garba Rikiji na jam’iyyar APC wanda ya samu kuri’u 52,495.

A mazabar tarayya ta Gummi/Bukkuyum, Injiniya Suleiman Abubakar Gummi na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 35,664 inda ya doke Ahmed Mohammed na jam’iyyar APC da ya samu kuri’u 35,058.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here