Ayarin motocin Babban Kwamandan Runduna ta 8 kuma Kwamandan Sashi na 2 na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Manjo Janar Bemgha Koughna, ya dakile wani mummunan harin kwanton ɓauna da ake zargin ‘yan kungiyar Lakurawa ne suka kai a kusa da Tudun Mayama.
A cikin sanarwar da aka fitar ta shafin rundunar a ranar Litinin, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar ta 8 sashi na 2 na Operation fansar Yamma Laftanar kanal Olaniyi Osoba ya ce harin ya faru ne yayin da ayarin motocin kwamandan ke kan hanyarsa ta kai ziyara ga sojojin da ke bakin daga a yankin.
Ya ce ‘yan bindigar sun bude wuta mai karfi kan ayarin motocin yayin da suke bi ta cikin dazuzzuka.
Sanarwar ta ce Manjo Janar Koughna tare da sojojinsa sun mayar da martani cikin gaggawa da tsari, inda suka kashe ‘yan ta’adda biyar tare da fatattakar sauran maharan.
Matakin ya tabbatar da tsaron ayarin motocin tare da dakile shirin maharan, tare da isar da sako mai karfi na gargadi ga kungiyoyin masu tada kayar baya a yankin.
Bayan artabun, sojojin sun yi sintiri a yankin inda suka kwato makamai da sauran kayayyaki masu yawa.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindiga kirar OJC guda daya, bindiga kirar PKT guda daya, bindigogi kirar AK-47 guda biyu, harsasai na AK-47 guda hudu, bel din harsasan PKT guda daya, harsasai masu girman milimita 12.7 da dama, jaka dauke da Naira 840,000, wayoyin hannu guda biyu, da babura guda biyar.
Sojoji na ci gaba da zama a yankin tare da sanya ido domin hana sake aukuwar hare-hare.
Sanarwar ta bayyana cewa Rundunar ta 8 na da kudurin kare fararen hula da kawar da barazanar ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.












































