An sake gano gawar mutum uku a ruftawar gini a Lagos

974e093a 3406 47b4 90ef ce7ba3745b76
974e093a 3406 47b4 90ef ce7ba3745b76

Hukumar bayar da agajin gaggawar ta Najeriya ta ce an samu karin adadi na wadanda suka mutu sakamakon ruftawar wani gini a birnin Legas.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta shaida wa BBC cewa an samu karin gawarwaki uku a yau Litinin yayin da ake ci gaba da aikin ceto a wajen da ginin ya fadi.

A ranar Lahadi ne dai ginin mai hawa bakwai da ke tsakiyar birnin ya rufta

Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin ruftawar ginin ba.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce kwamishinan tsara birane na jihar Dakta Idris Salaka ya yi murabus a wani matakin farko na sauya fasalin hukumar, an kuma gargadi duka sauran ma’aikatar hukumar da su girmama doka.

Faduwar gine-gine dai ba sabon abu ba ne a birnin Legas, inda ake zargin mazauna birnin da yin watsi da dokokin da hukumar tsare birane ta jihar ta gindaya kafin aiwatar da gini a birnin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here