Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi‘ yan leken asiri ne da ke ba da bayanai ga masu garkuwa da mutane.
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, SP Gambo Isah ya fitar wadanda ake zargin, Bilyaminu Ma’aruf ami shekaru 35, da Sani Umaru mai shekaru 40, sunyi kaurin suna wajen bada bayanani ga ‘yan fashi.
Karanta Wannan: Gwamnatin Tarayya Za Ta Biya Basussukan Ma’aikatan Kiwon Lafiya-Buhari
Sanarwar ta ce: “A yayin binciken, wadanda ake zargin sun furta cewa su ne suka kitsa garkuwa da mutane da yawa na yankin Dutsinma ciki har da na Amina Usman mai shekara 20, inda aka biya Naira dubu Dari Tara ga masu garkuwa, kuma an ba su Naira dubu ashirin a matsayin kason su na aikin da suka kista.
“Bugu da kari, sun kuma furta cewa sun bayar da bayanai ga‘ yan fashin da suka kai ga sace Amina Shu’aibu mai shekara 22 dake Dutsinma, wanda daga baya ta tsere daga hannun ‘yan bindigan, har da sauran irin wadannan garkuwa da mutane a yankin.
Ana ci gaba da bincike gameda lamarin, ” in ji sanarwar.










































