Gwamnatin Zamfara ta rufe gidajen rediyon Pride Fm, NTA Gusau bisa halartar gangamin taron gwamnan PDP

Matawalle new 2
Matawalle new 2

Gwamnatin jihar Zamfara ta rufe tashoshin gidajen talabijin na NTA da Pride FM da Gamji TV da kuma Al’umma TV a jihar bisa halartar tarukan siyasar dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP Dauda Lawal.

Rahotanni sun ce taron ya gudana ne a ranar Asabar a gidan dan takarar jam’iyyar PDP dake kan titin Gusau GRA zuwa Ring Road.

Kwamishinan yada labarai na jihar Ibrahim Dosara ne ya sanar da wannan mataki a gidan rediyon jihar a yammacin ranar Asabar.

Gwamnatin ta kuma umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yusuf Kolo, da ya kamo duk ‘yan jaridar da suka halarci taron.

Sanarwar rufewar tashoshin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Alhaji Ibrahim Dosara ya fitar.

Sai dai sun ce tashoshin ne suka keta dokar tsarin gwamnati ta aikin jarida.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Juma’a ne gwamnatin jihar ta ba da sanarwar dakatar da zirga-zirga a kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi, biyo bayan sake barkewar hare-haren ‘yan bindiga a kan al’umma.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, gwamnatin ta kuma bayar da umarnin dakatar da duk wani taro da ayyukan jam’iyyar.

“Bugu da kari, gwamnati ta dakatar da duk wasu harkokin siyasa a jihar har sai an samu wata sabuwar sanarwar.

“Haka kuma an hana tarukan siyasa cikin gaggawa,” in ji Mista Dosara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here