Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta sa ranar 17 ga watan Agusta don fara sauraron karar da Wike ya kai Atiku Abubakar.
An shigar da karar mai lamba (FHC/ABJ/CS/782/2022) a ranar 6 ga watan Yuli.
A safiyar yau Juma’a dai gwamna Wike ya ce shi bada yawun sa aka shigar da karar ba, kuma bai ma san wadan da suka shigar da karar ba.










































