Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum daya tare da raunata wasu biyu a wani hari da suka kai a unguwar Shola da ke jihar Katsina.
Harin dai na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan da ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai suka mamaye wani gari a Jihar.
Wani mazaunin yankin wanda ya tabbatarwa da gidan Talabijin na Channels faruwar lamarin ta wayar tarho ya ce ‘yan bindigar sun afkawa al’ummar ne da misalin karfe daya da rabi (1:30 am) na dare.

Ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu ma’aurata a harin da ya dauki tsawon sama da mintuna 30, inda ya ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Katsina domin kula da lafiyarsu.
Shola Quarters dai anguwa ce da ke bayan Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, kuma suna fuskantar hare-hare sakamakon ‘yan bindiga da ke kewayen yankin Bugaje a karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina.










































