Kafar ‘yan jaridu masu rahotanni kan al-amuran zamani NADIR, ta bayyana goyan bayan ta ga hukumar ci gaban Fasahar Sadarwa ta Najeriya NITDA, bisa yunkurin hukumar na samar da dokoki da zasu su sa ido a kan yadda shafukan sa da zumunta ke aiki, don magance matsalar yada labaran karya da tunzura aluma a kafafen sada zumunta.
NADIR ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da tayi yau Litinin a jihar Kano.
NADIR ta ce duk wani abu wanda ba ka-ida a cikin sa to akwai tarin matsaloli a tattare dashi, amma kowa duk sha-anin da yake akwai tsari da dokoki, tabbas za’aga fa ida a cikin sa.
Ta kara da cewa hukamr ta NITDA bawai tana kokarin dakatar da mutane bisa ‘yan cin bayyana ra’ayin su ne a kafafen sada zumun taba, illa kwai hukumar na kokarin tsaftace harkokin, domin magan ce yada labarain karya dana tunzura al-uma da ke faruwa a kafafin sada zumun ta na zamani.
NADIR ta yi kira ga ‘yan jaridu su cigaba da wayar wa jama’a kai akan yunkurin hukumar ta NITDA.










































