Arewa Radio 93.1 FM ta kammala wasan karshe na kakar gasar muhawara ta biyu mai wacce ke da nufin inganta tattaunawai, zurfafa tunani da fasahar magana a bainar jama’a a tsakanin daliban sakandare a Kano.
Gasar ta tattaro dalibai 16 daga makarantun sakandare daban-daban a fadin jihar, inda dalibai uku suka yi fice tare da samun kyaututtuka bayan makonni da dama na gasar.
Malama Hajara Ahmad Sani ta makarantar Samaru International School ta zo ta farko da maki 53.5 inda ta lashe Naira miliyan 1, sai kuma Malama Rukayya Muhammad ta Star Science College ta zo ta biyu da maki 47 inda ta samu Naira 700,000, yayin da Malama Ummulsalama Mustapha ta Government Girls Secondary School ta zo ta uku inda ta samu Naira 500,000.
Rahoton SolaceBase ya nuna cewa a wasan karshe Hajara da Rukayya sun yi muhawara kan taken: “Bangaren Lafiya Ya Kamata Ya Samu Karin Kasafin Kudi Fiye da Ilimi a Najeriya Dangane da Bukatar Yawan Jama’a.” ‘Yan takarar biyu sun bayyana hujjoji masu karfi, kwarin gwiwa da tunani mai zurfi a gaban alkalai da masu sauraro.
Da take jawabi a madadin Arewa Radio, Esther Isiaka, jami’ar sadarwar rukunin Arewa Radio da sauran tashoshin Cool FM da Wazobia FM, ta ce an tsara muhawar ne don kalubalantar dalibai su yi tunani fiye da abin da ake koyarwa aji tare da shirya su don jagoranci a nan gaba.
Ta bayyana cewa ko da yake Muhawara sabuwa ce a Kano, ra’ayin ba sabo ba ne ga kungiyar, domin an dauko shi daga shirin muhawara da Nigeria Info ke gudanarwa a birane kamar Legas, Abuja da Port Harcourt.
A cewarta, an gudanar da kakar farko a Kano a watan Nuwamba 2025, yayin da wannan da aka kammala yanzu ita ce kaka ta biyu.
Ta kara da cewa ana tantance mahalarta ne bisa tsarin gabatarwa, salo da kuma yadda suke mayar da martani, inda ta kara da cewa masu shirya gasar sun fi mai da hankali ga daliban da kansu ba makarantun da suke wakilta ba.
A nasa bangaren, Babban Sakataren na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Bashir Baffa Muhammad, ya ce gasar muhawar ta yi matukar burgewa kuma ya tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da mara wa irin wadannan shirye-shirye baya.
Ya kuma yaba wa Arewa Radio da masu tallafa wa gasar bisa goyon bayansu.
Hajara Ahmad Sani ta Samaru International School, wacce ta zo ta farko a gasar, ta gode wa masu shirya gasar da masu tallafawa bisa goyon bayansu. Ta kara da cewa kyautar da ta samu za ta zama abin da zai kara karfafa gwiwarta domin ta kara himma.
Haka kuma, Zainab Abdulmalik, Jami’ar Talla ta AA Rano Rice Mill Limited, ta ce kamfanin ya yi farin ciki da tallafa wa shirin, inda ta bayyana ilimi a matsayin jari mai muhimmanci da bai kamata a yi watsi da shi ba.
Ta ce kamfanin ya himmatu wajen tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta ilimi da ci gaban matasa, kuma ta yaba wa Arewa Radio bisa gayyatar kamfanin ya zama daya daga cikin masu tallafawa gasar.
Sauran masu tallafa wa taron sun hada da Muddassir and Brothers, Igwe’s Palace, IRA da Indomie.












































