SolaceBase Hausa
A kan hanyata ta zuwa makaranta, ina ganinsu kusan kowace rana.
Yaro ko yarinya ‘yar shekara bakwai ko takwas, a tsaye cikin zafin rana da kwando a hannu, suna kiran masu wucewa, wani lokacin suna murmushi, wani lokacin kuma suna da gajiya. Amma abu daya tabbatacce shi ne ba sa zuwa makaranta.
Wani rahoto da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya fitar a karshen mako ya ce Najeriya tana da kusan yara miliyan 18.3 da ba sa zuwa makaranta, adadi mafi yawa a duniya.
Rahoton ya ce jihohin Jigawa, Kano da Katsina wadanda ke Arewa Maso Gabanshin Najeriya, su ne kan gaba cikin jihohin da ke da mafi yawan adadi. Wannan ba abin mamaki ba ne.
Rahotan ya bayyana adadi ne kawai na abin da da yawa daga cikinmu muke gani kuma muke rayuwa da shi a kullum.
Yana da ban mamaki, kamar abu ne mai girma da ba za a iya misaltawa ba. Amma a gare ni, ba adadi ba ne ko lambobi ba kawai, shi ne wannan yaron da ke gefen hanya, haka zalika, ita ce wannan yarinyar da ke kasuwa. Su ne yaran da muke wucewa ba tare da yin tunanin irin halin da suke ciki ba. Kuma watakila wannan shi ne ainihin matsalar.
Mun koyi kallo, amma ba mu koyi gani ba.
Da yawa daga cikin wadannan yaran ba a boye suke daga al’umma ba, ana yawan samunsu a gefen hanya, kasuwanni, muhallin manyan makarantun gaba da sakadare har ma da ofisoshi, suna yin ayyukan hannu kamar wanke-wanke, aike-aike ko talla.
Sau da yawa ina mamakin yadda safiyarsu take, yayin da nake shirin zuwa laccoci, ina tattara littattafaina da tunanin ayyukan gida, me suke tunani a kansu? Rayuwa? Yunwa? Daga ina za a samu kudin gaba? A wane lokaci ne rayuwarsu zata dauki wata hanya dabam da tawa?
Rahoton ya yi magana kan talauci, rashin tsaro, da shingen al’adu, kuma wadannan gaskiya ne. Amma sama da duk wadannnan, akwai wani abu mai matukar tayar da hankali, da yawa daga cikin wadannan yaran ba a taba ba su wata dama ta gaske ba tun daga farko.
Idan ilimi tun daga kasa ga yara yana da muhimmanci kamar yadda masana ke fada, to hakan na nufin tsarin ya gaza musu tun kafin su kai shekarun da za su ma fahimci menene makaranta kuma duk da haka, rayuwa ta ci gaba.
Muna wuce su, muna saye daga wurinsu, wani lokaci ma muna yabon su da cewa “suna aiki tukuru,” ba tare da tambayar dalilin da ya sa yaron yake aiki tukuru haka ba tun farko. Akwai kuma wani abu da ba ma magana akai sosai, kuma wannan shi ne rawar da gida ke takawa.
Rahoton ya nuna cewa iyaye kalilan ne ke shiga cikin ilimin farko, iyalai da dama, yanke shawara game da makomar yaro ba koyaushe ake yin sa da ilimi a matsayin fifiko ba, kuma idan hakan ta faru, sakamakon ba ya zuwa nan take amma yana dawwama. Amma ina tunanin cewa wannan ya fi manufofi ko kulawar iyaye girma.
Magana ce kan abin da mu a matsayin al’umma muka saba da shi, domin gaskiya ita ce, wadannan yaran ba wai ba a iya ganin su ba ne, muna ganinsu kowace rana, kawai ba koyaushe muke tsayawa muna tunanin yadda rayuwarsu za ta kasance ba. Abin da har yanzu za su iya zama idan abubuwa suka canza.
Watakila ainihin bala’in ba wai yawan yaran da ba sa makaranta ba ne kawai, watakila shi ne cewa rashin kasancewarsu a aji ba ya kuma ba mu mamaki yadda ya kamata.












































