Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf a ranar Juma’a ya bada umarnin a gudanar da bincike kan zargin cire Naira Biliyan 1.5 daga kudaden ma’aikata da tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Abdullahi Musa, ya yi.
Gwamnan ya bayar da wannan umarnin ne yayin bikin ranar ma’aikata, lokacin da yake martani kan zarge-zargen da Shugaban Kungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kano, Kabiru Inuwa, ya gabatar.
Gwamna Abbba ya ce ya umarci Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG), Umar Faruq-Ibrahim, da ya kafa kwamitin bincike don duba zargin.
Ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta dauki mataki mai tsanani kan duk wanda aka samu da laifi kuma ta tabbatar da cewa za a dawo da kudaɗen.
“Na ji shugaba a jawabinsa yana magana kan zargin cewa tsohon shugaban ma’aikata ya kashe wasu kudade da suka kai Naira Biliyan 1.5. Nan take da na ji haka, na kira SSG kuma na bayar da umarni cewa a kafa kwamitin bincike nan take don duba wadannan zarge-zargen.” In ji gwamnan.
“Ina so in tabbatar muku cewa duk wanda aka samu da hannu, gwamnati za ta dauki mataki mai tsauri don tabbatar da an mayar da kudaden.”
Gwamnan ya ce gwamnati ta biya Naira Biliyan 32 daga cikin Naira Biliyan 48 na bashin fansho da kudn rasuwa da ta gada.
Ya yi alkawarin biyan ragowar Naira Biliyan 16 kafin karshen mulkinsa.
“Na gaji bashin fansho da kudaden rasuwa da suka haura Naira Biliyan 48, kamar yadda shugaban Kungiyar Kwadagon Najeriya ya fada a jawabinsa.
“Ina so na fada kuma cewa wannan ya jefa masu ritaya da iyalansu cikin matsanancin wahala, kuma kamar yadda shugaban ya bayyana, ta hanyar kokari na musamman da dorewa, mun biya Naira Biliyan 32 zuwa yanzu daga cikin jimillar Naira Biliyan 48.
“Muna kuma da niyya da yardar Allah, mu share ragowar a cikin wa’adin wannan gwamnatin nan.”
Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa ta kuma kafa manyan cibiyoyi da nufin kula da jin dadi da kwararrun ma’aikatan gwamnati.
“Kafa Hukumar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ya tabbatar da cewa ayyukan ma’aikatan kananan hukumomi yanzu sun yi daidai da ka’idoji da ci gaban da ake samu a sauran bangarorin aikin gwamnati.”
A cewarsa, gwamnati ta kuma inganta jin dadin masu ritaya ta hanyar kara mafi karancin fansho daga Naira 5,000 zuwa Naira 20,000, ci gaban da ya inganta yanayin rayuwar tsofaffinmu sosai a cikin watannin da suka gabata.
Tun da farko, Shugaban NLC, Kabiru Inuwa, ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta binciki zargin da ake yadawa na Naira Biliyan 1.5 kan tsohon shugaban ma’aikata.
Inuwa ya kuma yi kira ga gwamnati da ta magance bambancin albashi tsakanin ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha domin karfafa gwiwar ma’aikata da kuma tabbatar da ka’idar daidaito. (NAN)












































