Gwamnatin Kano na ci gaba da farfaɗo da wuraren shakatawa yayin bikin Sallah Gwamnatin

FB IMG 1774179606868 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta sake jaddada ƙudirin ta na kare muhalli da inganta jin daɗin al’umma, inda take ci gaba da aikin farfaɗo da muhimman wuraren shakatawa a faɗin birnin yayin da al’umma ke bikin karamar Sallah.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a ranar Lahadi, kwamishinan muhalli da sauyin yanayi, Dakta Dahir M Hashim, ya bayyana cewa ya kai rangadi domin duba yadda aikin ke gudana a manyan wuraren shakatawa guda huɗu a rana ta biyu ta Sallah, yana mai cewa wannan na daga cikin shirin sabunta birane na gwamnati.

Hashim ya ce wuraren da a baya aka mayar da su wuraren kasuwanci yanzu gwamnati ta ƙwato su, kuma ana sake gina su domin su koma wuraren kore da kuma wuraren shakatawa.

Ya bayyana cewa wannan shiri na da nufin samar da wuraren wasa masu tsaro da zamani ga yara da iyalai a faɗin Kano.

Ya ƙara da cewa waɗannan wurare da aka karkatar da su zuwa kasuwanci a baya yanzu an dawo da su, kuma ana maida su wurare masu ƙawa da kore masu armashi domin amfanin jama’a.

Kwamishinan ya kuma ce aikin ya yi daidai da hangen nesa na gwamna Abba Kabir Yusuf a ƙarƙashin abin da ya kira “Green Mandate”, wanda ke da burin faɗaɗa samun tsababbun wuraren shakatawa ga jama’a.

A cewarsa, gwamnatin na shirin kammala wuraren shakatawa guda 10 masu cikakken aiki a cikin birnin kafin bikin babbar Sallah mai zuwa, domin inganta rayuwar al’umma.

Hashim ya jaddada cewa aikin na tafiya yadda ya kamata duk da lokacin bukukuwan Sallah, yana nuna aniyar gwamnati na ba muhalli muhimmanci.

Ya kuma taya al’ummar Kano murnar Sallah a madadin ma’aikatar, yana fatan zaman lafiya da haɗin kai da kuma ci gaba a jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here