Osinbajo, Atiku da sauran manyan baki sun halarci bikin nadin Olubadan na 42

Ibadan
Ibadan

 

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubarkar, na daga cikin fitattun mutanen da suka halarci nadin Oba Olalekan Balogun a matsayin Olubadan 42 na Ibadanland.

Sauran manyan baki da suka halarci taron sun hada da Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti, Gwamna Dapo Abiodun na Ogun, mataimakin gwamnan Osun, Benedict Alabi da Lucky Aiyedatiwa, mataimakin gwamnan jihar Ondo.

Daga bangaren sarakuna akwai Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III; Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi; Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar; Olugbo na Ugbo, Oba Fredrick Obateru Akinruntan sai kuma jakadan kasar Sin a Najeriya, Cui Jiauchun.

Haka kuma akwai tsohon gwamnan jihar Oyo da Otun Olubadan, Cif Rasidi Ladoja da tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas, Femi Pedro, wanda ya wakilci Asiwaju Bola Tinubu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an fara taron ne da misalin karfe 11.14 na safe tare da rera taken kasa, wakar jihar Oyo da kuma wakar Ibadan.

Kiristoci da Musulmai ne suka gudanar da addu’o’in bude taron da kuma addu’ar gargajiya ta Araba Awo na Ibadanland.

Har ila yau, Moshood Ayanyemi, Atookowagbowo, ya jagoranci sauran mawakan Ibadan, inda suka tarbi baki da masu yi mata barka da zuwa bikin ta hanyar gargajiya.

Sai dai kuma an shigo da Olubadan na Ibadanland na 42 da misalin karfe 11.50 na safe, inda daga nan ne dukkan sarakunan gargajiya, malaman addini, shugabannin kungiyoyi daban-daban na Ibadanland suka kai gaisuwar ban girma ga Oba Balogun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here