Sule Lamido ya yi barazanar kai ƙara idan aka hana shi takardar neman kujerar shugaban jam’iyyar PDP

Sule Lamido new new 750x430

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon ministan harkokin wajen ƙasa, Sule Lamido, ya bayyana cewa zai kai ƙarar jam’iyyar (PDP) idan aka hana shi damar samun takardar neman kujerar shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Lamido ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar a ranar Litinin, sannan ya ziyarci sakatariyar jam’iyyar da ke birnin Abuja domin sayen fom, amma ya ce ya tarar da ofishin da ake sayar da fom ɗin a rufe.

Ya bayyana cewa ofishin sakataren shirya harkokin jam’iyya na ƙasa, Umar Bature, wanda ke da alhakin sayar da fom ɗin, yana kulle tare da rashin wani bayani daga manyan jami’an jam’iyyar.

Lamido ya ƙara da cewa an shaida masa daga bisani cewa fom ɗin yanzu yana hannun gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda ke shugabantar kwamitin shirya taron ƙasa na jam’iyyar.

Ya nuna takaici da lamarin, yana cewa bai dace jam’iyyar ta kasance cikin ɓoyayyun al’amura ba ko ta nuna son kai ga wasu mambobi, inda ya ce idan bai samu fom ɗin ba, zai garzaya kotu domin kare haƙƙinsa.

Lamido ya musanta zargin cewa wasu gwamnonin jam’iyyar sun ƙi goyon bayansa saboda alaƙarsa da jam’iyyar ADC, yana mai cewa shi ne cikin waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen gina jam’iyyar tsawon shekaru 25 da suka wuce.

Ya kuma yi gargaɗi kan yadda wasu ke raina tsarin cikin gida na jam’iyyar, yana cewa hakan na iya lalata tsarin dimokraɗiyya a cikin jam’iyyar kafin babban zaɓen 2027, tare da jaddada cewa PDP ba za ta ci nasara ba sai ta kiyaye tsarin da kundinta ya tanada.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here