Majalisar Malamai ta Kano ta sanar da cewa za a gudanar da (Salatul Ga’ib) sallar jana’izar marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya rasu a jiya Juma’a.
A cewar sanarwar da shugaban majalisar Malam Ibrahim Khalil ya fitar, an shirya gudanar da sallar ne da misalin karfe 2:00 na rana a masallacin Umar Bin Khaddab da ke Gyadi-Gyadi a Kano.
Ya kuma tabbatar da wannan tsari tare da yin kira ga al’ummar Musulmi da su halarta da yi wa marigayin addu’a.












































