Ma’aikatar zuba jari da kasuwanci da masana’antu da jam’iyyun gama kai ta jihar Kano, ta kaddamar da sabon kwamitin riko da zai kula da harkokin kungiyar Kasuwar Kantin Kwari domin dawo da zaman lafiya da hadin kan ‘yan kasuwar.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar, Mohammad Nura Yusuf ya sanya wa hannu a ranar Litinin din makon nan ce ta bayyana hakan.
Matakin dai ya biyo bayan wani taro da kwamishinan hukumar Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya kira da nufin magance rikicin shugabanci da ya dabaibaye kungiyar.
SolaceBase ta ruwaito cewa, a cewar sanarwar, kwamitin sulhun wanda ya kunshi manyan masu ruwa da tsaki da dama sun amince da shigewa gaba wajen magance matsalar.
Sabon kwamitin rikon da aka kafa ya kunshi mutane kamar haka:
1. Sharu Na Mallam – Shugaba
2. Shehu Muhammad Tariga – mataimakin shugaba
3. Sharhabilu Abdulkadir – Sakatare
4. Abubakar Kabir Babawo – Ma’aji
5. Naziru Rabiu Abubakar – Jami’in Hulda da Jama’a PRO
6. Bello Mukhtar Gaya – Mamba
7. Alhassan Abdu Mukaddas – Mamba
8. Sha’aibu Anto – Jami’in walwala
9. Anas Sani Gwammaja – Jigo a kwamitin watau Ex-Officio











































