By Aminu bala madobi
Hukumar Hisba ta jihar Kano, ta cafke wani matashi mai shekara 26 wanda ya ce zai sayar da kansa saboda talauci ya dame shi.
A ƙarshen makon da muka yi bankwana da shi ne hoton Aliyu Na Idris ya karaɗe shafukan sada zumunta yana ɗauke da kwali rubuce da buƙatar wanda zai saye shi kan naira miliyan 20.
A jawabinsa ga manema labarai, babban Kwamandan hukumar Hisba ta Kano Sheik Muhammad Haroon Ibn Sina, ya tabbatar da kama matashin yana mai cewa matashin ya aikata haramun.
”Mun kama shi ranar talata har ya kwana a hannunmu saboda abin da ya akaita haramun ne a addinin Musulinci, ba ka da damar sayar da kanka a kowanne hali ka tsinci kanka” in ji kwamandan.
Aliyu Idris wanda tela ne, ya ce yana cikin matsalar kuɗi, don haka ne ya yanke shawarar sanya farashin naira miliyan 20 tare da shan alwashin yiwa duk mutumin da ya saye shi hidima tuƙuru.
Kafin kama shi, Aliyu ya bayyana manema labarai a Kano cewa: ”Na yanke shawarar sayar da kaina ne saboda talauci, idan na samu mai saye, na shirya bai wa iyayena naira miliyan 10, na biya naira miliyan biyar a matsayin haraji ga gwamnati, naira miliyan biyu ga duk wanda ya taimake ni na samu mai saye na, sai na ajiye sauran don amfanin yau da kullum.










































