Ƴan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 10 a Kaduna

bandits
bandits

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da dalibai kusan guda 10 a karamar hukumar Kachia na jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ta ce gwamnatin jihar ta samu labarin afkuwar lamarin daga wajen hukumomin tsaro a jihar.

Rahotanni da aka samu sun ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin a wata makarantar sakandare da ke karamar hukumar.

Aruwan ya ce ba a tabbatar da hakikanin wurin da lamarin ya faru ba, amma ya ce suna jiran cikakken bincike domin tabbatar da hakan.

Ya kuma ce gwamnati za ta fitar da sanarwa a hukumance idan aka kammala tattara bayanai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here