Wakilan ɓangarorin da ke yaƙi da juna a ƙasar Sudan sun hallara a ƙasar Saudiyya domin tattaunawar sulhu ta gaba-da-gaba a karon farko tun bayan ɓarkewar yaƙin a tsakiyar watan Afrilu.
Za a yi tattauanwar ne wadda Saudiyya da Amurka suka ɗauki nauyinta tsakanin ɓangaren sojin ƙasar da dakarun tsaro na RSF.
Yarjejeniyoyin tsagaita wuta da dama a baya, ba su yi nasara ba tun farkon fara yaƙin makonni da suka gabata.
Duka ɓangarorin sun ce za su amince da tsagaita wuta domin bai wa fararen hula damar ficewa daga yankunan da yaƙin ya fi nƙamari.
A ranar Asabar ne ministan harkokin wajen Ƙasar Saudiyya Faisal bin Farhan ya tarbi wakilan ɓangarorin biyu ya yin da suka isa ƙasar domin tattaunawar sulhun.
Ya ce yana fatan tattaunawar za ta kawo ƙarshen rikicin tare da maido da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.
Janar Mohamed Hamdan Daglo wanda ke jagorantar dakaruyn RSF ya bayyana a shafinsa na Tuwita cewa rundunar RSF ta yi maraba da matakin tsagaita wutar domin samun damar kai tallafi cikin ƙasar.
Ya kuma ce RSF a shirye take domin mayar da mulki hannun farar hulka a ƙasar.