Zulum ya bai wa masu yi wa ƙasa hidima a Borno tallafin rage raɗaɗi

Zulum 750x430
Zulum 750x430

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya ce zai raba wa matasan da ke yi wa ƙasa hidima a jihar su 1,215 tallafin 30,000 kowanensu domin rage raɗaɗi.

Zulum ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci sansanin horar da masu yi wa ƙasar hidima ranar Asabar a Maiduguri, inda ya ce zai ware naira miliyan 36.4 domin bai wa matasan tallafin.

Haka kuma gwamnan ya bai wa masu yi wa ƙasar hidima buhun shinkafa 100 da na wake 10 da jarkar man girki 10 domin yi wa matasan abinci a lokacin da suke karɓar horon na mako uku.

“Ina son faɗaɗa rabon tallafin rage raɗadi ga masu yi wa ƙasarmu hidima da ke jiharmu. kowane mutum guda a cikinsu zai samu naira 30,000, za kuma a tura muku kudin ne ta asusun ajiyarku na banki”, in ji Zulum.

Ya kuma buƙaci matasan da su yi biyayya ga dokokin sansanin wajen zama lafiya tare da aiwatar da duka ayyukan da suka wajaba a kansu, domin ciyar da ƙasarsu gaba.

Gwamnan ya kuma bayyana jin dadinsa ga gwamnatin tarayyar ƙasar wadda ta inganta tsaron jihar domin bayar da dama da matasan domin su yi hidimar ƙasa a jihar.

An dai kwashe shekaru masu yawa ba tare da horar da masu yi wa ƙasaa hidima ajihar ba, sakamakon hare-haren ƙungiyar Boko Haram.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here