
Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani basaraken gargajiya a garin Sagamu da ke Ogun a ranar Talata.
Karanta wannan: Yanzu-yanzu: Betta Edu ta isa Hukumar EFCC don amsa tambayoyi
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa ’yan bindigar mutum uku sun harbi basaraken ne a wani waje.
Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Karanta wannan: Gwamnati ta dakatar da biyan mafi karancin Albashi-TUC
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Abiodun Alamutu, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da ba da tabbacin cewa za’a cigaba da bincike gami da kama wadanda suka kai harin.












































